NAINAH (HASKENA)
Episode_________40----44
Admin 002
Dahiru Muhammed Faila
Rijau Niger State
@Whatsapp 08039127523

Da Sauri Ya dauketa ya nufi mota da ita, Fahad Ya
bude masa ya shiga Yana rungume da ita,
Rauda wani kallo ta Watsawa mufeedah kafin taja
dogon tsaki ta shiga Tata motar Tabi bayansu,
Mufeedah ko ajikinta
"sai nayi ajalinki Nainah indai baxaki bar min mijina ba
taja tsaki ta fice,
"Fahad be fast jinin na xuba sosai kada ya qare, bana
so na rasata,
"abokina Baka ga saurin da nake bane? Kayi haquri ynxu
xamu isa,
Ya tsura mata ido, kallonta yake sosai yana jin sonta da
tausayinta, ya cire rigar jikinsa ya rage daga shi sai
singlet yasa rigar yana tare mata Jini,
Sun iso asibitin itama Rauda ta iso, a tare suka fito
yana dauke da ita a hannunsa, Kai tsaye emergency aka
nufa da ita,
Sai safa da marwa yake hannuwansa goye a bayansa,
'brother ka kwantar da hankalinka Nainah xata sami
sauqi harta tashi, Fahad yayi xugum yana kallonsa
Suna tsaye gurin nurse ta fito,
"patient din na buqatar Jini, cos ta xubar da Jini sosai,
Mus'ab Ya tafi aka gwada nasa akayi sa'a yayi dai dai
suka diba suka sama ta bayan sun mata dinki,
A waya ya kira Ya sanarda hjy Duk abinda Ya faru, ranta
ya baci sosai bataji dadi ba hr gida taje ta sami
mufeedah tayi mata fada kamar me kafin ta xo nan
asibitin,
Hr lokacin bata Farfado ,
Hjy tace kaje gida Mus'ab baxaka mana yawo da singlet
a asibiti da Jini ba,
Hjy *haskena* ce fa, _you want me to go and leave
her_,
"oh my goodness, ta fada hade da dafe goshinta,
Nainah ce fa Mus'ab, u forget abinda ka gayamin akan
Nainah, ka manta mgnr mu,
Idanunsa sukayi jawur,
Ta matso kusa dashi a bayansa,
"Duk naga ka cnxa lokaci Qalilan Duk saboda Nainah,
Karka cemin ynxu kana son Nainah yar rainon sulaimi
ne,  _you luv her, don't you?_
_"who mother? no it's not like that I dnt love Nainah but
I never said nainah_
_I'm your mother you can't lie to me,you told me you
never love Nainah ,you will never cry for Nainah, my
words hurt you right? Today Mus'ab is crying for
Nainah, my son is pretending to luv Nainah,ka manta hr
addu'a kayi min akan Nainah, you see my eyes are
clear son_,
Ya juyo Kacokan yana kallonta
_'I'm not pretending Mother, Nainah ce *haskena* an
you know it, Nace bana son Nainah ne cos I dnt know
her, why ol dis mother, I love Nainah, I love Nainah and
I still love Nainah_, itace *hasken xuciyata hasken
idaniyata*, ya fada idanunsa akanta,
Fahad da Rauda na soma dariya, hajiya ma dariya take
"so nake Naji da bakinka ne kamar ynda kace baka son
Nainah da farko yau kana furta kana son Nainah,
Olryt hajiya xnje nayi wanka, you take care of
*haskena*,
Ta riqo hannunsa,
Son Karka kula mufeedah olready na sameta gida nayi
mata fada, kishine na mata ka kyaleta pls,
'I will mother, amma Wannan shine na farko na qarshe
Idan ta qara taba *HASKENA*, xata bar gidan, ya juya
Ya fice da Sauri batare da Ya saurari amsar taba,
Fahad Ya Kalli agogon hannunsa ya fice yana fadin
'sister xn tafi Anjima kadan xn shigo,
Shikenan Fahad ka gaida surayya, ya fice yana
murmushi bayan yayiwa hajiya sallama,
*
Farfadowarta yayi dai dai da shigowarsa, ta dafe kanta
da hannunta tana yatsina fuska alamar xafi🤕,
Hajiya da Rauda a tare sukayi mata sannu, ba wanda Ta
amsa daga ciki Illah idanunta data maida ta lumshe
badan komai ba sai Dan ganin Mus'ab a dakin,
Rauda Tace Alhamdulillah tunda ta tashi ni xnje gida
Nabar jabir gun mai aiki kuma ina so nayi wanka,
Hjy tace Ki saukeni gidan hajiya Mariya Anjima driver
xai daukoni,
Suka juya suna mata sannu ta amsa a hankali kamar
wadda akayiwa dole,
Ta juyo a hankali tana kallonsa shima idanunsa akanta,
'Ya jiki
Tayi shiru hade da dauke idanuwanta akan nasa,
'kiyi haquri da abinda mufeedah tayi maki,
Nan ma shiru ba amsa,
'Ga abinci me xan xubo miki,
Shiru.. Ya tsura mata ido
'Nainah, ya kirata cikin husky voice dinsa, ta juyo da
idanunta akansa ba tare da ta amsa ba,
'you hate me right?
Ta gyada Kai tana kallonsa da oily eyes dinta dake
rikitashi,
Jikinsa nayi sanyi did *haskensa* Mean it? Why did
she hate him,
Yayi shiru kansa a qasa,
*
 Kwana biyu Alhamdulillah ta
sami sauqi hr lokacin mufeedah bata jeba, yana kula da
ita sosai duk da Nainah na kauda kanta akansa, itafa
bata sonsa kuma batasan dalili ba,
Rauda ta qoqarin xuwa dubinta akai akai da haka har
sukayi sabo mai tsananin tsakaninsu, sukan xauna
suyita hira tsakaninsu hr da dariya Mus'ab na gefe xai
xuba mata narkakkun idanuwansa yana kallon dimple
dinta, Rauda na matuqar Tausayinsa sosai, Idan Rauda
batanan Shida ita zaman kurame ne da kallon kallo
shiyasa yake son zaman Rauda asibitin Dan ta riqa
dariya Yana kallonta,
Suna cikin haka majeed da bahijja suka xo dubinta, tuni
sun shirya kansu sun amince da junansu,
Kallo daya tayi masu taji faduwar gaba ta dauke
dubanta garesu hr lokacin da suka qaraso suna mata ya
jiki bata tanka ba,
Rauda na sallah, Mus'ab na daga gefe Ya kalleta a
sanyaye
'Nainah bakijiba suna miki Ya jiki,
Idanunta akansa ta saki wani malalacin murmushi
'na jisu dear jiki Alhamdulillah and what else,tayi far da
ido tana kallonsa, kusan rikicewa Ya tashi yi,
'he can't believe it, idanunsa da kunnuwansa sun
qaryata shi, how comes Nainah Ke kallonshi haka, did
she call him her dear, nooo he can't believe it, sai ya
sakar mata murmushin da bai Kai xuciyarsa ba,
Rauda ta sallame sallah tana kallonsu, Nainah ta fara
son Mus'ab ne ko kuma Dan ganin su bahijja ne?
Bahijja ta xauna kusa da ita hade da riqo hannunta,
'Nainah did I deserve what I see in your eyes, kin
tsaneni saboda namiji Nainah, why Nainah?
Ta xare hannuwanta daga nata,
"me kike son gani a idanu na, luv or what, kin amince
kin Karbi soyayyar wanda Ya cutar da Xuciyar qanwarki,
you know it Anty bahijja ba wanda nake so kamar sa
but why kike tarayya dashi, Meyasa kike son wanda
qanwarki keso, ta soma kuka...
Lokaci daya Mus'ab da Rauda suka tashi majeed Ya
juya xai fice ta Kira sunansa,
"Karka dauka ina son ka ne a ynxu, bana sonka mijina
nake so ina gayawa Anty bahijja rashin dacewarta akan
abin da tayi, ta juya Tana kallon bahijja
"xaki iya tfy nagode,
Bahijja ta ware idanunta sosai akan ta
'Nainah you are sending me away from you,  ta gyada
Kai tana kallonta
'yes....
Rauda taja hannun bahijja suka fita, sun Dade a waje hr
majeed kafin ta dawo ,
Mus'ab, hajiya tayi min waya ynxu akan Skul, 2 days
now bakaje Skul ba, Fahad Ma daxu Naji yana ma mgnr
kuna da lectures yau,
Sister Idan Nainah taji sauqi Anyi discharging dinta
xanje,
Nooo yakamata kaje am with her xn kula da ita,
Ya xauna fuskarsa ba Walwala alamar baxai jeba, ta
ciro wayarta ta gayawa hajiya baxai jeba, yana ji
wayarsa na ringing yasan hjy ce yaqi dauka,
Nainah ta janyo wayarta, txt ta tura masa, yana xaune
yaji shigowar txt a wayarsa kamar baxai duba ba ganin
number *yar raino* ,kamar ynda yayi saving number😂
ta, da Sauri Ya buda
_"kaje lectures din'ka sister will take care of me._
Ya dago da sauri Yana kallonta, fuskarta a daure take
kamar ba ita ta tura txt din ba,
Ya tashi yana kallon Rauda,
'sister am going, ki kula pls,
'A dawo lfy, ya Kalli Nainah kamar xai mata mgn sai
kuma ya fasa ya fice da Sauri.

Bayan kwana biyu akayi discharging dinta suka dawo
gida,
Komai daga sashenta Ya cnxa an sanya mata sabo, ga
masu aiki birjik kamar irin na mufeedah, dakinta ma an
cnxa komai kamar nashi dakin illah banbancin colour an
qayata nata dakin da white and purple, murmushi Tayi
Tana cije labbanta
'sai kace xn tabbata a gidannane, yake wahalar da
kansa haka very soon am living ba xn iya xama da
mutumin da bana so ba,
Ta xame Dan kwallin kanta,gashinta Ya xubo a
kafadunta ta xauna bakin gadon tana kallon dakin,
kyawunsa da tsarinsa Ya Birgeta,
'can't believe, Wannan dakin nawane, Nima Inada masu
aiki xn bada umarni kamar Anty mufeedah, komai xaa
riqamin, Idan akamin girki bana so fa, ta tunxure
bakinta hade da dafe goshinta
'oh bana so, I dnt like it a girkamin wani, ta saki
murmushi,😊
Idan suka min mopping baiyi ba, how I am going to
talk to them, ta daga kanta sama kamar mai naxari, oh
I remember ynda Anty mufeedah keyi,
'Ke Wannan wane mopping ne haka da Kissa Idan
baxaki iya ba sai in koreki in nemo wani, nooooo ta
girgixa kanta
"ba haka xn ce ba, Dan Allah Ki qara mopping Wannan
bai yi ba, ta saki murmushi😊
'correct Nainah ,ta fada ta baya ta kwanta a
luntsumemen gadon,
Duk Wannan abin da take Mus'ab na tsaye bakin qofar
dakin hannuwansa rungume a kirjinsa Ya xuba mata
narkakkun idanuwansa, yaga tana mgn tana murmushi
amma baiji me take nufi ba, a tunaninsa Nainah is
happy with the room, yaga murmushi a fuskarta did she
mean she is happy with the house, sai yaji yana so
agama Wancan gidan da ake Dan yakai Nainah aciki
baisan wane farin ciki xatayi da gidan ba, yana son
ganin murmushi a fuskarta, yana son ganin qaramin
bakinta na motsi dimple dinta Ya lotsa it shows her
beauty, ya juya Ya fice yana murmushi.
*
Kwanan ta biyu bata sanya mufeedah a ido ba, Mus'ab
kuwa kusan kullum xai shigo dakinta ganin lfyr Jikinta,
'kina da matsala?
'ba inda Ke maki ciwo?
'me kike so?
'ina kike son xuwa?
'kina buqatar kudi?
'me xan siyo maki Idan na fita? Duk amsar dayace
babu shima fuskarta ba Walwala take amsa masa, zai
juya a sanyaye ya fice, baisan mexaiyi Nainah ta saki
jiki dashiba, bai San Meyasa bata sonshi ba, ya kaiwa
Rauda Wannan complain,
'Nainah bata San komai akan aure ba Mus'ab Kai xaka
koyarda ita sannan akwai Kunya atare da ita, ya girgixa
kansa
'nooo sister ba Kunya a tare da Nainah, she hate me
sister, tell me what to do.
' kanada gardama Mus'ab, nainah ta taso ba mahaifiya,
yakamata ka gane, inna baxata xaunar da ita ta koya
mata wani abu dangane da rayuwa ko Ta aure ba,
sannan bahijja ma kanta Tana buqata ka tuna basu da
lokacin kansu daga tallah sai bauta da reno tell me
taya Nainah xatasan ynda xata Tafiyar da Rayuwar ta
you have to teach her ko kana tunanin majeed xai koya
mata ne,  ina so ka fahimci wani abu Nainah batasan
miye so ba hr ynxu, majeed shaquwa ce dake
tsakaninsu hr take ganin so ne,
'ka koya mata Yanda xata soka Mus'ab, ka xauna tare
da ita ko bata so, kuyi hira tare, ku ci abinci tare, kuyi
wasa tare, ku yi barci tare, Meyasa ma nake Gayama
kasan komai ai,
'sister amma ai bn koyawa mufeedah hakan ba, kafin
muyi aure kina ganin she takes care of me, sannan
matan dake Sona a waje bn koya masu ynda xasu soni
ba rushing dina suke fa ki tambayi Fahad.... Ta katsesa
Nainah dabance da mufeedah, Nainah batayi ilimin
mufeedah ba, Nainah batada wayewa kamar ta
mufeedah, Nainah batayi wayon mufeedah ba sannan
Nainah ta taso cikin rashin gata da kulawa, a ynxu
Nainah Ke tasowa kanta na wayewa, ka Barta ta shiga
cikin mutane qawayenta she will have more experience
ka fahimceni,
Ya gyada Kai yana kallonta,
Gobe ka Kaita inda surayya matar Fahad Ta yini a can hr
dare, ka Kaita inda hajiya, kaxo da ita nan, ka Kaita gun
umman mufeedah, Idan xaka iya ka Kaita family house
ma, ka Kaita inda frnds dinka masu aure xata rinqa
ganin ynda ake tfyr da rayuwar Aure,daga nan ma
shaquwa mai qarfi xata iya shiga tsakaninku ,you get
me?,
Ya riqo hannunta,
'proudly to Have you sister, kina Raina Ya sumbaci
hannunta,tayi dariya sosai ta tashi Tana fadin xn shiga
kitchen Abban jabir yana hanya,
'oh nama tuna munada contract da shi akan wani fili,ta
juyo tana kallonsa
'bai taba gayamin ba ,me xaiyi da fili kuma?
'Amarya xai miki.... Ta soma dariya
 Ai ni kishiya bata bani
tsoro niba irin mufeedah bace tazo mu xauna,
Mus'ab ma dariya yayi ya tashi yana laluben makullin
motarsa a aljihunsa yana fadin
'Nima baxan gaya miki ba tunda bai fada miki ba inajin
yana so ya baki surprise ne.
Ga dambun nama ka kaiwa Nainah in yamata dadi Idan
taxo xn koya mata,
Ya Karba yana murmushi
'sister kina ganin xata Karba,
'me xai hana ta Karba ,dayan kuma ka bawa mufeedah,
'suna Godiya sister but ni fa?
'Kaci tare da Nainah ai yanada yawa.... Murmushi kawai
yayi ya fice...
*
San da ya iso harabar gidan yayi parking Ya fito suka ci
Karo da Inna xata shiga gidan, yasan ba dan Allah Ta xo
ba sai ya tare ta,
'Inna Nainah bata gidan?
'ina taje ta tambaya tana kallonsa,
'na Kai ta saloon,
'miye saloon kuma? 🙄
'inda ake gyaran gashi,
'Chabdi Wannan gashin akwai mai iya gyaransa ne
kasan ynda gashinta yake kuwa, inta sakeshi haka take
komawa kamar aljana, dama kasa scissors ka rage
matashi , ya kalleta da mamaki ba abinda yafiso a jikin
Nainah kamar gashinta da dimple dinta,
'tor kayi shiru ni xan tafi,
'a gaida baffa,
'baxaka ban kudin keke napep bane,
'banda kudi ynxu, ya juya Ya fice ta bishi da kallo kafin
tayi kwafa ta fita daga gidan,
Sai da ya kaiwa mufeedah nata kana ya nufi sashen
Nainah,
Ya shiga dakin hade da sallama Tana xaune a qasa
tana sanya sajan a hannuwanta bayan ta gama sanya na
qafafu, ta sanya na hannu daya bata San ynda xata
sanya dayan ba,
Ta amsa sallamar batare da ta dago ba,gashinta Duk ya
xubo Ya rufe mata fuska tana son tattara gashin ba
hannu Ya matsa kusa da ita ya tattaro shi bayanta, Silbin
gashin da tsantsinsa yasa Ya manta duniyar da yake sai
ya cigaba da Jan gashin,
'Enough pls, muryarta ta katse shi, ya saki gashin yana
fadin
'am sorry pls Nainah, ya dawo gabanta Ya xauna ya
miqa mata dambun,
'sister tace na kawo maki dambun nama ne,
Ta saki murmushi Tana kallonsa Karo na farko da ta
soma kallonsa da murmushi kusan rikicewa Ta tashi yi,
'ina son dambun nama, sau daya na taba ci😮a Skul
dinmu, kayiwa sister Godiya Naji dadi,
'Rilly? Ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa, ya
gyara xamansa😂,ta gyada Kai
'sister tace xata koya miki Idan kina so, kuma xn iya sa
a koya maki a gidama tunda kinaso,
'thanks ta fada bayan ta maida hankalinta a lallen da
takeyi,
'in my life ban taba ganin mace na sanyawa kanta Lalle
ba sai akanki, ina ganin su mufeedah ana xuwa ana yi
masu ne sannan ban taba ganin irin Wannan naki ba su
naga Idan Anyi masu xanen basa rufewa da Leda kuma
flower ake xana masu asanya masu wani abu ja,
Ta Dan dubeshi kafin ta dauke kanta
'Kai ashe kanada surutu haka, yayi murmushi kawai
'tun a gida ma Nike sawa da kaina Idan anti bahijja bata
nan, Wannan sajan ne ba iri daya da wanda kake nufi
ba,ta miqo masa yatsunta
Help me I can't, wani dadi yaji Nainah ta sanyashi yayi
mata abu, ya ajiye wayoyinsa da makullan sa ya riqo
hannunta kamar Karen tankada😂saboda rashin Qiba,
'kamar Wannan hannun haka xakayiwa yatsun, koma
barshi bana so ka bata hannunka da Ja xan barshi haka,
'no Nainah Kibari xn maki karki damu, ya soma Samata
kamar gaske Ya iya, bata ankara da abinda yake ba sai
da ta juyo taga Duk ya game yatsun da Tafin hannun Ya
shafesu da Lalle hr bayan hannun kamar dungu (lallen
tsohuwa😂),ta xare idanu sosai hade da sakin yar
qara ta fisge hannun tana kallonsa a fusace, shima
kallon ta yake da mamaki baisan dalilinta na Wannan
Ihu ba hade da fisge hannunta.....

Hawaye suka xubo mata, duk Yabi ya Rikice
'what Nainah?
Ta dubeshi da manyan idanuwanta
'ji fa, haka nace kayi, a yatsu kawai nace fa dubi ynda ka
rufe duka tafin hannu, dungu ne fa na tsofaffi irin su
Inna,
Ya soma dariya yana kallonta,
Ke ashe haka kike da surutu, kin taba mgn mai tsayi
kamar Wannan? Ta kafa masa idanuwa cike da takaici,
ya tashi yaje Ya debo ruwa a bowl, ya sanya hannunta a
ciki yana wankewa, kusan minti goma yana murxa
hannun cikin ruwa,
Ta soma qoqarin xame hannu
'xaka cnxa min kalar fata ne, ya dube ta
'Oh sorry Nainah ,ya sanya towel yana goge hannu Ta
duba har ya fara Ja ta shagwabe fuska kamar xatayi
kuka, ya Kama kunnuwansa duka yana kallonta
'Afuwan Nainah don't mean to hurt you.
Tana juya hannun tana kallo
'is OK,
Ya xame Ya xauna yana fadin
'thank you *haskena*, ta dan dubeshi,
'ka fita xn tashi naje na wanke lallen I know ynxu Ya
gama yin ja
'let me help you Nainah, kafin tayi magana ya
sungumeta yayi toilet da ita sai wutsil wutsil take da
qafafu tana Kiran,
'No I dnt Nid your help ,bai saurareta ba sai a toilet Ya
ajiyeta, ya xaunar da ita ya riqo qafafunta yana cire leda
'oh no bana so pls kabarni xn iya, Karka Je ka lalatamin
qafa again, bai saurareta ba Ya soma wankewa ba ynda
ta iya ta xuba mishi ido tana kallon cutie face dinsa, ya
tsurawa qananan qafafunta ido da sukayi jawur, bai
taba ganin lallen da yayi kyau kamar na qafafunta ba
ynda yayi jawur a qaramar qafarta
'hey you what are you looking, ya dubeta yana
murmushi
'see Nainah yatsun qafafun mu are the same dogaye
ne,
'I see..., ya riqo dayan hannun daya Ya wanke ta tashi
Tana murmushi Tana kallon qafafunta ita kanta sun
Birgeta sun mata kyau ta dubeshi
'tnks friend,
Yaji wani dadi Nainah ta kirashi friend kenan xata soshi
after yasan xata kirashi lover, husband, honey, darling
and so on.
Ashe da gskyr sister da Tace Ya yi kusanci da ita
shaquwarsu xata janyo soyayyarta gareta,
Ta fito tana murmushi Yabi bayanta hr lokacin Tana
kallon qafafunta da hannunta daya, Idan ta Kalli dayan
da Ya
Bata sai yaga ta yatsina fuska da haka yaga ta janyo
dambun tana ci haiqan kamar mai yunwa,
'Nainah sister tace xamuci tare, ta Dan dube sa tana
ware idanuwanta
'I thought kace sister ta Baka dambu ka kawo min ne?
'tace Muci tare,
'Olryt gashi, ta taso ta kawo masa ya hada hannunta da
robar dambun yana kallon
'Wannan lallen yamin kyau Nainah let me snap it, ya ciro
wayarsa yana daukar hannunta da qafafuwanta ta Karba
tana dubawa
'wow yayi kyau friend xaka nunawa baffa inayi Lalle ina
nuna masa a gida,
'I promise you Nainah xn nuna masa, kuma xn nunawa
sister da hajiya,
Tayi murmushi kawai tana cigaba da cin dambun.
*
Ta fito Sanye da doguwa Riga ta atampha tayi matuqar
yi mata kyau, ta nufi kitchen....
Oh nooo ta fada kamar xatayi kuka komai bata iya
amfani dashi ba aciki, stove ma batasan Yanda xata
Kunna shi ba, ta taso ta sami ana girki da murhu a
gidansu ta juya Ta fita can sashen masu aiki
Hajjo ta gani tana cin abinci, tana ganin Nainah ta soma
murmushi,
'yar arxiki mai qashin arxiki me kikeso,
'hajjo ina so Kidawo sashe na da aiki, duk masu aikin
can ba wanda nayi sabo dashi, sai ki riqa tayani hira
kina nuna min ynda ake amfani da kayan kitchen I dnt
know anything hajjo,
Hajjo tayi shiru
"Nainah Kema Kinsan hajiya baxata bari ba, baxata
Barni na miki aiki ba xama ta iya korata daga gidan, kiyi
haquri pls,  Nainah ta shagwabe fuska kamar xatayi
kuka,
'nooo hajjo Nafita buqatarki Nafita sanin darajarki,
Inaso na miki gata kamar ynda kika taimakeni a lokacin
da banda kowa, kina cikin mutanen da baxan manta
dasu ba a rayuwata, bana manta alheri komai
qanqantarsa, ni dake Duk masu nema ne, baki taba
haihuwa ba kisa a Ranki Ke mahaifiyata ce, bnda uwa
nayi maraicin uwa Ki daukeni ya' ni xan dauke Ki uwa
pls hajjo,
Hajjo ta soma sharar kwallah
'nagode Nainah amma Ki Barni anan xn kula dake,
'noo hajjo you must follow me, taja hannunta,
mufeedah dake Jinsu ta Fisgo Nainah ta hankadata
gefe,
Kee👈🏾Ki shiga taitayinki dani, kifita harkata
kidaina shiga sha'anina sannan kifita hanyar duk masu
aikina Inba haka ba Wlhy xn Karyaki,
'Anty kibar hajjo ta xauna tare dani, xn baki wata mai
aiki a maimakon ita, pls Anty she is my mother.....
'Ke har kin isa Kibani mai aiki, who are you? Me kike
dashi? Me kike Taqama dashi? Inaji ma a gidanku
Muke ciyarda su, ko kin manta Ke wacece mai rainon
sulaimi fa,
Ta juya Tana hawaye a falonta taci Karo da Mus'ab
yana nemanta, ganin ta shigo tana hawaye ya sanyashi
rikicewa,
'me ya sami Nainah? Ko mufeedah ce, sai ya fita acan
Ya sami mufeedah tana xagin hajjo
Mufeedah ya kira sunanta da qarfi
'why kike xaginta haka, ta haifeki fa, tayi masa wani
kallo tana kallon hajjo
"lol funny you Mus'ab, Wannan xaka ce ta haifeni oh
God,
'me Kikayiwa Nainah?
'au ta Kai qarata kenan, Tor taxo ta kwata baxan bada
ba,
'menene ya tambaya yana kallonta, me *Haskena* keso
kika hana mata,
'tun kafin taxo gidannan rainon sulaimi nake tare da
hajjo sai ynxu Dan Munafurci xata ce hajjo ta koma aiki
sashenta saboda sunyi sabo.
Ya dubi hajjo
'hajjo kina son xama da Nainah? Ta gyada Kai tana
kallonsa a tsorace take da mufeedah,
'daga yau kin koma aiki acan, *haskena* must get what
she wants, kinsani na kuma gaya miki  ki fita harkarta,
kibarta ta wala a gidan mijinta, ki Barta taji dadin
rayuwarta, kidaina sa tana xubar da hawayenta, Idan
kina son mu daidaita Ki daina taba, *haskena* ku duka
matana ne tana da right akan komai kamar ynda kike
dashi ,bn Takuraki ba kidaina takura  *Haskena*
mufeedah ya fada cikin tsawa yana kallonta, ta juya ta
fice shima Ya fice hajjo ta tattara kayanta Tabi bayansa,
Nainah na ganinsu ta dubeshi da murmushi,
Friend hajjo xata xauna dani? Ya gyada Kai yana
kallonta ya dubi hajjo
'kije bayan gidan akwai masu aikinta acan, tayi Godiya
ta fice,  Nainah ta fada jikinsa tana dariya
'tnks friend, yayi shiru yana kallonta yana jin wani abu na
masa yawo a jiki Ya dora hannunsa a lallausan gashinta
yana shafawa,
_farin cikin ki shine nawa *haskena* I will do my best to
make you happy_, ki shirya ynxu xamuje inda baffa.
Ta soma tsalle..
'thanks friend, ta fada toilet a gurguje Ya bi ta da kallo
yana sauke ajiyar xuciya, kafin ya juya Ya fice,
Ta gama shiryawa tana qoqarin sanya Sarqa Ya shigo
shima cikin nasa shiri, ta juya Tana kallonsa yayi
matuqar kyau ta saki murmushi shima yayi mata
murmushi,
'hey friend you look 👌🏻,hr cikin Ransa yaji dadi, ta
miqa masa Sarqar tana fadin
'help me pls, ta juya masa baya, ya sanyo Sarqar ta
gabanta Ya xagayo da ita bayanta, Tana kallonsa ta
madubi, Ya tattara gashin ya sakeshi ta gabanta kana ya
sanya mata Sarqa,
'tnks ta fada a hankali amma Kai kafiye kallo, is like
everything is new to you.
'yes Nainah you are correct,  everything is new to me
amma na Nainah, ta miqo masa qaton ribon tana fadin
saura gashin,
'how Nainah baxan iya Kama shi ba,
'xaka iya try your best, ya Kama gashin wani na fita da
kyar ya iya hadesu wuri daya Ya karbi ribon din Ya sanya
mata, sai yayi sukuku bai kamu da kyau ba,
'oh noo friend ta xame ribon din bai kamu da kyau ba
nafiso ka tsuke sosai Dan kwali fa xan daura,
Ya saki ajiyar xuciya Ya gaji sosai, ya Kama gashin Karo
na biyu ya Kama sosai ya tsuke sai da ta saki qara😂
Ya saki da Sauri yana fadin
'sorry Nainah do it by yourself, ta qara juyawa
'Nidai ka Kama ahankali bada xafi ba,
'oh Allah help me, ya sake kamo gashin a Karo na uku
da kyar yaga ya kamashi dai dai ya sanya ribon,
'I hope is OK Nainah '
'yes ta fada tana tufke gashin kafin ta laulayashi kamar
ganwo akanta🙄,
'Nainah you have to be fast magrib ta kusa,
'Olryt friend, ka ciro min gyale na da takalmina kafin na
gama kwalliya,
'Nainah kina nufin xaki qara wani kwalliya ne, oh my
goodness, you  are ok like this u look beautiful,
'OK ciromin gyale acan ta nuna masa, Den you check
my shoes,
Ya dafe kansa kawai kafin ya juya.

A tare suka fito Yace ta jirashi sashen mufida ya
nufa,
Xamu fita tare da Nainah ko xaki Je?
Ta girgixa kanta batare da ta kalleshi ba,
'did I hurt you Mufeedah saboda Nainah, sai a lokacin
ta juyo tana kallonsa, idanunta sun kawo kwallah, ya
dawo ya xauna kusa da ita hade da riqo hannunta,
'saboda nabawa Nainah hajjo ne mufida, kiyi haquri
nasan ban kyauta miki ba is just I can't control my self
akan Nainah amma baxan qara ba kiyi haquri pls,
Ta xame hannunta batare da tayi mgn ba, har ya qare
surutunsa Ya fita ya sami Nainah hr ta gaji da tsayuwa
sai tsaki take
'sorry Nainah, ya bude mata motar ta shiga Tana
tunxure baki,
Tafiya sukayi mai Nisa kafin su iso gidan, shi Ya Bude
mata motar ta fito, suka shiga cikin gidan,
Baffa na ganinsu Ya soma murmushi, bahijja da majeed
da Yasir na xaune suna kallo,
Inna ana uwar daka tanajin muryar Mus'ab tayi xuruf ta
fito
Nainah ta gaida baffa da Yasir kana ta dubi Mus'ab
dake tsaye,
'friend..., ya juyo yana kallonta,
'xo nan, yaje Ya xauna kusa da ita, kallonta kawai suke
ta canxa sosai ta qara kyau da haske, bahijja taje ta
kawo masu ruwa Nainah bata kula ba.
Inna Tace Nikam ban taba ganin yarinyar dake xuwa
gaida mahaifanta babu Leda ba keko yar tsaraba
babu,aure baiyi albarka ba🙄? ,
Duk ba wanda Ya kulata kasancewar sun Saba da
halinta amma Mus'ab yaji wani iri Duk da yaga Nainah
bata damu ba sai faman hira take da baffanta,
'Nainah an sanya ranar auren bahijja da majeed nan da
wata daya in Allah Ya yarda,
Gabanta Ya fadi komai nata Ya tsaya cak wani abu taji
ya taso Ya tokare mata xuciya, tayi shiru tana wasa da
awarwaron hannunta,
'a nijar xaayi bikinsu saboda al'adun mu kin sani ai, ta
dago tana murmushi Ta dubi Mus'ab
'let's go friend,
'na dauka sai anijima za.... Ta katsesa
'let's go please
'OK Nainah, a tare suka tashi ta dubi mahaifinta.
'baffa xamuje, ina so naje inda sister, ta juya batare da
taji amsar Saba, Mus'ab Ya ciro kudi Ya ajiye masa
yafita, su majeed sukaje rakiyarsu tun kafin su qaraso ta
shiga motar ta rufe da qarfi, Mus'ab yayi masu sallama
ya shiga motar.
'Ban San Meyasa Nainah ta tsaneni ba bahijja ba haka
nakeso xumuncin da ita ya Dore ba,
'kabarta fushinta na wani lokacine tana ganin kamar
munci amanar tane.
Nainah da gske xakije inda sister ynxu,
Ta girgixa kanta Tana kallonsa da oily eyes dinta dana
soma kwallah, ya cigaba da tuqin sai da suka iso
harabar gidan ya juyo Kacokan yana kallonta
'Meyasa kika tsaneni, dame majeed Ya fini, kyau ko
kudi? Meyasa kike fushi da yayarki saboda xata auri
majeed? Tayi shiru
'Kinsan ynda nake son Ki Nainah? Kinsan ynda na
haukace akanki? They call me crazy Kaita cos of you
haskena, they even laugh at me, sun so su maidani
mahaukaci da sunga mace xasu riqa Kiran *hasken
kaita*,ina sonki tun bansan Ke wacece ba, cos of you
na cnxa halina, ina son talakawa, ina girmama mutum
nadaina Girman Kai da izza ko a Skul, pls Nainah Ki
soni ko kadan ne, ya fada kamar xaiyi kuka ,
Ta balle murfin motar ta fita da Sauri, hajiya ta soma cin
Karo da ita,
'ina Mus'ab
'yana xuwa,
'ina neman ku,  atare suka isa falon mufeedah suka
xauna mufeedah na xaune idanunta sun Kumbura
saboda kuka,
Hajiya ta dubeshi fuskarta ba Walwala
'Mus'ab, mufeedah wacece a gareka?
'matata hajiya,
'Nainah fa?
'itama matata ce,
'Tor Meyasa kake nuna banbanci akan su, dame Nainah
tafi mufeedah, Meyasa kake fifita Nainah akan
mufeedah, mufeedah yar uwarka ce ko ka manta?
'mother am trying my best, bansan me nayi ba ynxu.
'why kake takurawa mufeedah akan Nainah shi nake son
sani, danme xaka kwace mai aikinta ka baiwa Nainah
sannan danme kake fita da Nainah bada mufeedah ba
gata ta fita kome?  Ina so kaji tsoron Allah ka kuma
kwatanta gsky tsakanin matan ka duk cikinsu ba wadda
ta fi wata kuma bana son banbancin da kake nunawa,
'mother mufeedah ta gayamiki qarya, sai danace taxo
muje taqi, mgnr mai aiki na bata haquri ai ta barwa
Nainah.
'baxai yiwu ba mai aikin mufeedah ce kuma na dawo
mata da Abarta kowa Nada nashi kuma kowa Ya tsaya
matsayinsa bana so sonkai son understand?
Ya gyada kansa
'but mother.... Ta katsesa
'is OK gsky nake Fadama ,ya tashi jiki a sabule ya fice,
nan hjy ta hada Nainah da mufeedah tayi masu nasihohi
kana tabar gidan,
Nainah tasha kuka kamar ranta xai fita, abu biyu na
hade mata
'xamanta gidan bataso Baa sonta, sannan auren majeed
da bahijja kuma wai hr xaa Je nijar Amata Biki kenan
anfison bahijja akan tane, bahijja tafita matsayi kome,
itama xataje nijar inda yan uwanta su kwatar mata
yan'cin ta a raba aurenta da Mus'ab tunda bata sonshi
batason matarsa shima qarya yake mata baya sonta irin
na majeed xai mata tnk God tasan hanya da wayonta
Sunje Bikin qanwar baffa.
Da Wannan tunanin ta tashi ta hada kayanta a trolley da
Duk abinda xata buqata da kudaden da take da,
Mus'ab na tare da Fahad a Wannan lokacin Yana
gayamasa damuwarsa,
'yana cikin tsananin buqata mufeedah taqi ta bashi
haqqinsa hr sai ya saki Nainah kuma shi baxai iya barin
Nainah saboda mufeedah ba,
'Tor ita Nainah sai ka xuba mata ido kana kallonta kana
da mata biyu ka kasa biyawa kanka buqata.
'abokina Nainah yarinyace batasan Wannan abin ba
bnma San Yanda xn tunkareta da abin ba dama ace
tana so nane.
'ina Wannan pills din dana Baka used it mana kasamata
a drinks ta sha kabiya buqatarka Inba haka ba xaka
kashe kanka a banxa.
'you want me to rape Nainah, Fahad?
'bashi nake nufi ba tasha pills din tukunna sai kabi da
ita a hankali ynda baxata gane ba,
 Yayi shiru kafin yace
shikenan,
Fahad Yace Inada mata biyu baxan ci amanar Kai na
ba, kai mufeedah ma yar rainin wayo ce Wlhy ita
yakamata kayiwa da qarfi,
'noo ai kasanni bana roqon mace akan Wannan abin sai
ta rainani, ido xn xuba mata xata nemeni Nima xn
Rama,
Fahad yayi murmushi
'surayya tayi akwai haquri Allah Ya biyata,
'Amin that is how I want my Nainah to be.....
Sanda ya iso gidan bayan yayi wanka ya shirya cikin
kayan barci masu kyau da taushi ya nufi sashen
mufeedah, ya xauna yana kallon sulaimi dake barci
'my lovely baby olways sleeping ita bata gajiya da barci,
ya sumbaci goshinta, mufeedah tayi murmushi
Ya dubeta
'are you ready ko hr ynxu kina kan bakanki?
'yes ai Nagayama Idan ba ka rabu da Nainah ba baxan
taba yarda da Kai ba, a zatonta xai rarrasheta ya roqeta
ga mamakinta sai taga ya tashi yana latsar wayarsa
'Olryt mufeedah cwt dream, ya fice ta bishi da kallo
kamar xatayi Ihu Ya dawo Dan tana cikin buqata itama.
Sanda ya fita dakin fridge ya nufa Ya tsurawa drinks din
ido kafin ya xabi cock ya dauko Ya balla maganin kadan
baison ya mata over,ya tabbatar da Ya gauraye kana ya
nufi dakin Nainah dai dai lokacin ta fito wanka tana
daure da towel, Karo na biyu da Ya qara ganinta da
towel kallonta yake sosai Duk ilahirin tsikar jikinsa tashi
take tun da Ya dora idanunsa akan cinyoyinta,
Ta gyara gashinta tana kallonsa,
'hey why are you looking at me like that,
Mus'ab Ya sauke ajiyar xuciya kana ya xauna bakin
gadon yana fadin
'put on ur Clothe Nainah kixo xamuyi hira yau,  ta Dan
dubeshi
'am not inviting you Friend inajin barci,
'OK ga cock na kawo maki kisha,
'noo ni bana sha
'pls Nainah ko kadan ne am your friend right?
Ta Karba ta Kurba hade da ajiyewa akan mirrow ta
cigaba da shafa mai yana kallonta tana sha, ta gama ta
janyo rigarta lokacin ta fara ganin dishi dishi idanunta
na lumshewa, lashes dinta masu tsawo suna hadewa da
junansu ta nunosa da hannunta tana tangadi da rigar a
hannunta,
'hey you, me ka bani.., am feeling some how, kasheni
xakayi? Kaci amanata friend, ta fadi ragwaf a jikinsa, ya
rungumota yana jijjigata
'noo Nainah ba kashe Ki xanyi ba, baxan ci amanarki ba
Ke nake so ba jikinki ba na haqura Nainah Ki tashi pls
baxanyi komai dake ba sai da amincewarki, ya soma
hawaye, ya janyo cock din yasha yana fadin mu mutu
tare Nainah you can't go and leave me.
Da kyar ya iya gyara mata kwanciya a qirjinsa, yana
rungume da ita sai faman surutai yake shi Kadai hr barci
Ya Daukeshi,
Asubar farin ita ta soma farkawa, idanunta sai
lumshewa suke barcin bai saketa sosai ba, fuskar
Mus'ab ta soma cin Karo da ita ta tsura mashi ido tana
kallonsa kafin ta shafa fuskarsa,
'friend is handsome and..... sai ta soma tunanin abinda
Ya faru Jiya ta tashi da sauri Tana kallon Jikinta Yanda
suke kwance tamkar wasu masoya,
'nooooo ta fada da Sauri ta tashi ta sanya kayanta ta
janyo trolley dinta hr xata fice ta juyo ta kallesa da Sauri
ta Je ta dauko Biro da paper tayi rubutu akai kana ta
dunqule ta ajiye akan mirrow ta gyara masa
kwanciyarsa taja masa blanket ta fice da Sauri.

10:00am kukan wayarsa na soma Farfado dashi
daga nauyayyen barcin da yake,
A hankali yake bude idanuwansa suna sake lumshewa,
kukan wayarsa ba ta daina ruri ba, a hankali bakinsa Ke
motsi, ni kaina badan na Kai kunnuwana saitin bakin shi
ba baxanji me yake fadi ba,
'Nainah! Nainah are you alive? Nainah taimakeni intashi,
Nainah come closer, please Nainah.
Kiran wayarsa na tsinke Baa jima ba ta sake ringing, hr
cikin kansa yake jin kukan wayar da kyar ya iya daga
hannunsa ya janyo wayar ya Kara a kunnensa,
Mtsew Fahad yaja dogon tsaki
'Kai malam saboda dadin mace kanaji ana kiranka
baxaka daga wayar ba,
A hankali Ya furta
'Fahad barciiiii
'mtsew ni ba Wannan ba naje Skul an Sanya mana
exam nxt wk ,Kai kaji mugunta pls I thought Wannan
semester bamu Dade da farata ba ko?
Da kyar Mus'ab Ya tashi yana murxa idanuwansa sosai
'Kai abokina bnda wasa
'joke apart Kaita ynxu haka ina Skul nayi mamakin ma
bnganka ba, dan Allah ka shigo ynxu akwai lectures,
'oh ni bana fargaban exam din Fahad amma baxan iya
fitowa lectures ynxu ba cos pills Dinnan dana sha Jiya
bai sake Niba,
'oh God Tor Waye Yace kasha,mtsew Ya tsinke wayar
cike da takaici yana fadin mayen Mace.
Mus'ab Ya duba baiga Nainah ba Ya saurara a toilet ba
motsinta ,ya fito Ya nufi falonta, kitchen, bedroom,
sitting room, E.T.C Duk batanan, har wajen masu aikin
gidan Duk ya bincika Babuta  hankalinsa nayi matuqar
tashi,
🗣Nainah 🗣Nainah 🗣Nainah yake Kiran sunanta
da qarfi, ko ina ana jiyosa ,mufeedah ta fito tana fadin
'me ya sami Nainah?
'ina Nainah banganta ba pls ki nemomin Nainah,
'Subhanallah Ta Fada Ta Juya Da Sauri Ta Nufi indasu
hajjo tana tmbyr Nainah, nan da nan gidan na rude,
Ya kira hajiya Ya gayamata cos Dad baya nan kana ya
kira Rauda
'sister, sister.....
'Trouble Mus'ab menene haka why are you shouting my
name xaka fasa min dodon kunne ne?
'sister banga Nainah ba, na tashi ban ganta ba, help me
sister Nainah ta gudu ta Barni da gaske take sister she
mean it ta tsaneni haka har xata iya guduwa ta Barni
😢,
'Ya Salam,ta fada jikinta a sanyaye mai Nainah Ke nufi,
why did she hate brother like this, me yayi mata,
Meyasa take wahalar dashi haka, Meyasa take son
maidashi mahaukaci Duk son da yake mata?
'ina xuwa Mus'ab ka kwantar da hankalinka xamu ganta,
ta tsinke wayar cike da haushin Nainah a ynxu,
Sai safa da marwa yake acikin gidan idanunsa sunyi
jawur, ya nufi dakinta ya soma bincike sai alokacin Ya
lura ba kayanta Qalilan ne ta bari Ya daki drawer kamar
Ya fashe da kuka,

(believe me karkuga laifinsa yana
jinta ne a xuciyarsa, kun san ynda so yake)

Ya dawo yana dube dube kamar mai neman wani abu
haka ya koma xararre shi Kadai a dakin, paper da tayi
rubutu ya gani *Mus'ab*,jikinsa na rawa ya dauka ya
soma warwarewa
_Am sorry friend, you d your best to make me
happy, you are such a nice person I can't forget you in
my life, am so sorry, sorry pls friend,nasan koda xaka
sami Wannan takardar tuni na Dade da yin Nisa a nijar,
xnje yan uwana su kwatar min yan'cina gareka da baffa
na Yimin auren dole, Karka Kira Nainah butulu mai
manta alheri nooo bana cikin masu mantashi komai
qanqantarsa, nasan xakace ka taimaki Nainah da yan
uwanta, you do this and that, ban mantaba, mufeedah
ce mai sonka take kishinka kayi haquri da matar ka
tafini sonka, ina Jiran takardata, Nagode._
*HASKENKA*
Xufa na soma karyo masa ya soma ball da Duk abinda
Ke dakin, Ya Farfasa mata mirror, duk ya yamutsa
gadon dama dakin, komai ta samu jifa yake dashi da
haka Rauda ta shigo ta samesa da Sauri taje ta
rungumesa,
'Mus'ab don't be crazy cos of Nainah,who is she? Me
take dashi dame tafi sauran matan, akwai mata
Wadanda na fita a Garinnan Mus'ab, why ol dis?
 Ta riqo fuskarsa
'look Mus'ab Ya kamata ka manta Nainah ka fita
rayuwarta tunda bata sonka, ka Barta ka sami wata
Mus'ab, kasami maccen da xata soka and make you
happy,
'sister baxan iya ba, Nainah ce kawai, ya miqa mata
takardar Yana fadin Nima xn bita sister xnje nijar yau,
ya fita da Sauri, Tabi takardar Tana karantawa kafin ta
yardata Tabi bayansa,
Gidan baffa suka nufa a rude ya sanardashi komai
hankalinsa dana bahijja ta tashi sosai, Inna kuwa kamar
ta xuba ruwa a fako tasha takeji,
Baffa Yace bahijja da majeed su shirya suje can nijar
din tare da Mus'ab daga nan suma Ayi masu Bikin aure
acan sannan su dawo da Nainah,
Mus'ab Ya kira hajiya Ya sanarda ita, bata ce komai ba
ta tsinke wayar, ya kira Fahad yana gayamishi,
'Baka da hankaline Mus'ab, nxt wk fa exam kana so kayi
Asara ne saboda macen da bata sonka?
'Nafiso so na rasa exam din akan na rasa Nainah Fahad
you know it.
'Tor wai ita kadaice mace a duniyarnan?dame tafi
sauran ne? Ya kamata ka dawo cikin hayyacinka kasan
me kakeyi, ni Dakai hr ita kun soma bani haushi, ya
tsinke wayar cike da takaici.
'you see Mus'ab no supporter, ya kamata ka haqura da
Wannan yarinyar kabata takardarta pls Nima a ynxu
haushi take bani, hajiya ta kira bata ji dadin abinda
Nainah tayi ba hrtace ka sauwaqe mata.
'shikenan sister xn saki Nainah xn haqura da Nainah, I
will be a man, xan dawo ainihin *Mus'ab Mohd Kaita*
dina,idan naje yau tace bata Sona xn bata takardarta,
Rauda ta kalleshi da tausayawa
'Allah xai Baka wacce tafi Nainah, mufeedah ta isheka
Mus'ab.
Majeed Ya fito yana fadin
'Baffa Yace abar tfyr hr Gobe Kafinnan na gama hada
kayan da xnje dasu na auren dama komai a kammale
yake,
Rauda Tace shikenan ma da yafi.
Washe gari suka daga xuwa nijer, Mus'ab, Majeed da
Bahijja kawai Yasir bai sami damar xuwa ba saboda
lectures din shi.
Inna na ganin ba kowa a gidan daga ita sai baffa tasa
kai ta fice da takardun gidan da suke ciki wanda Mus'ab
Ya basu,
Tafiya tayi ta sayarda gidan🙄,haka baffa na xaune
yaga maza na shigowa suna duba gidan kafin su fita bai
fahimci komai ba,
Miliyan biyu inna ta Karba hannunsu kudin gidan kana ta
nufi inda ake buga jaridu cike da farin ciki, dama Nace
sai nayi kudi sai duniya tasan dani, haka tasa aka buga
mata Jarida da hotonta akai ta washe baki an rubuta
akai *Hajiya shekara d Millionaire*, aciki kuwa labarinta
ta bada na qarya, Yanda akayi tayi kudi ynxu, ynda
tasha wahalar nemansu da dai sauransu,
Haka taxo ta cillawa baffa Jarida daya har lokacin Yasir
bai dawo makaranta ba, ta kwashi kayanta tana dariyar
qeta ,sai da masu gidan suka xo Karba take masa
bayani,
Kusan suman tsaye yayi
'shekara kina tsoron Allah kuwa, ina xakije da haqqinmu,
'ai ni shikenan burina Ya cika duniya xata sandani,
xakaga ynda xaa riqa nuna ni a T. V ,xn fara haraka da
manyan mutane Nima Dan haka ka sallameni,
'ynxu ina kike son naje nida Yasir, ina kikeson mu
xauna?
'Wannan matsalarkace ka bani takardata kana batamin
lokaci,
'kije Allah baxai Barki ba Allah na tare da Duk wanda
aka xalunta, nida ya'yana uku da kikaci amana sai kinga
sakayya na sakeki saki uku,
'Ayurrrrrrriiiiiii tafi nono fari, Saduwar Alheri ,
'kada Allah ya sake Sada fuskokinmu Wannan rabuwa ta
har abada ce ban marmarin sake ganinki mace irinki
azzaluma.
Taja akwatinta da sauran kayan da ta sata na bahijja ta
fice tana dariya.
Baffa kuwa masu gida suka fito dashi komai bai Dauka
ba, haka ya nufi bayan wani masallaci Ya xauna dafe da
qirjinsa saboda Ciwon da yake masa ga wani jiri da
yake gani, hawaye kawai Ke xuba a idanuwansa kafin
wani lokaci Ya soma tari sosai... 😢

Dahiru Mohammed Faila
08039127523

Comments